Shugaba Buhari ya tura wakilai zuwa Bauchi domin yiwa jama'a jajen iftila'in da ya afka masu

Shugaba Buhari ya tura wakilai zuwa Bauchi domin yiwa jama'a jajen iftila'in da ya afka masu

- Shugaba Muhammadu Buhari ya tura wakilai zuwa Bauchi don yin jaje

- Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne zai jagoranci tawagar tare da Direkta Janar na NEMA

- Hukumar NEMA ya fara shirye-shiryen kai kayan Agaji ga al'ummar da iska da gobara ta yiwa barna

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya jagoranci tawagar wasu ma'aikatan gwamnatin tarayya zuwa jihar Bauchi don yin jaje ga al'ummar Jihar bisa iftila'in da ya afka musu ya iska mai karfi da gobara.

Shugaba Buhari ya tura wakilai zuwa Bauchi domin yiwa jama'a jajen iftila'in da ya afka masu

Shugaba Buhari ya tura wakilai zuwa Bauchi domin yiwa jama'a jajen iftila'in da ya afka masu

Hadimin shugaban kasa a fannin kafafen yadda labarai, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya bawa manema labarai a fadan Aso Villa da ke Abuja.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen saboda tsoron harin ISIS

Rahottani sun ce iskan ta lalata gidaje 1,505 mafi yawancin su a babban birnin Jihar inda mutane takwas suka mutu kuma wasu mutane 120 suka jikatta.

Kazalika, an samu afkuwar gobara a garin Azare wanda ya lalata kasuwar garin.

Shehu ya ce wadanda ke cikin tawagar gwamnatin tarayyan sun hada da Direkta Janar na Hukumar bayar da agajin gagawa NEMA, Alhaji Mustapha Maihaja inda ake sa ran sai duba irin barnar da iskar tayi.

Sanarwan ta ce, "Tuni nema ta tattaro kayayakin agaji daga dakunan ajiya da ke Damaturu da Yola saboda rabawa wadanda iftila'in guguwar iska ta same su."

A wani sakon da ya bayar a ranar Litinin, Shugaba Buhari ya jajanta wa al'ummar guguwar da gobara ta shafe su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel