Nasara kan Boko Haram: Yan gudun hijra akalla 2000 sun koma muhallansu

Nasara kan Boko Haram: Yan gudun hijra akalla 2000 sun koma muhallansu

A yau Talata, 19 ga watan Yuni yan sansanin IDP na Bakassi a Maiduguri sun fara komawa muhallansu da ke karamar hukumar Guzamala na jihar Borno.

Yan gudun hijran su kimanin 2,043, wanda suka kunshi iyalai 378 sune Karin farko da za su nuna niyyar komawa muhallansu domin cigaba da rayuwa yadda aka saba na noma da suna da kuma wasu al’amuran yan da kullum.

Nasara kan Boko Haram: Yan gudun hijra akalla 2000 sun koma muhallansu

Nasara kan Boko Haram: Yan gudun hijra akalla 2000 sun koma muhallansu

Tiyata kwamandan Operation lafiya dole, Manjo Janar Rogers Nicholas, ya bayyana niyyar babban hafsan sojin kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai, na tabbatar da cewa yan gudun hijran da ke da niyyar komawa gidajensu su koma domin cigaba da rayuwa.

Ya kara da cewa kwamandan soji, gwamnatin jihar Borno, da shugabannin karamar hukumar Gizamala ne suka hada kai wajen shirye-shiryen komawansu.

Janar Nicholas ya kara da cewa hukumar tsaro ta karo karfin tsaro kuma zata kaddamar da atisayen sharan daji domin kaddamar da noman damuna a Gudumbali

Ya bada tabbacin cewa yan gudun hijran zasu cigaba da samun tsaro a muhallansu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel