Tabbas: Shugaba Buhari zai sanya Hannu a kan Kasafin Kudin 2018 a gobe Laraba - Fadar Shugaban Kasa

Tabbas: Shugaba Buhari zai sanya Hannu a kan Kasafin Kudin 2018 a gobe Laraba - Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Kasa ta bayar da tabbacin cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 da misalin karfe 12.00 na tsakar ranar Laraba ta gobe.

Kakakin fadar Mista Femi Adesina, shine ya bayar da wannan tabbaci cikin wata sanarwa da ya gudanar a ranar Talatar da ta gabata yayin ganawa da manema labarai a babban Birnin Kasar nan na Abuja.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, tun a ranar 13 ga watan Yunin da ta gabata ne hadimin na shugaban Kasa ya bayyana cewa shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 cikin wannan mako.

Legit.ng ta fahimci cewa, sanarwar Mista Adesina ba ta bayar da tabbaci dangane da ranar da shugaba Buhari zai sanya hannun kan kasafin kudin na Bana.

Tabbas: Shugaba Buhari zai sanya Hannu ga Kasafin Kudin 2018 a gobe Laraba - Fadar Shugaban Kasa

Tabbas: Shugaba Buhari zai sanya Hannu ga Kasafin Kudin 2018 a gobe Laraba - Fadar Shugaban Kasa

Majalisar Dattawa ta kara wani kaso cikin kasafin kudin zuwa N9.12trn sabanin N8.612trn na yadda shugaba Buhari ya gabatar tun a watan Nuwamba na shekarar 2017 da ta gabata.

KARANTA KUMA: Rikici: Rayuka 2 sun salwanta yayin kallon 'Kwallon 'Kafa ta gasar Kofin Duniya

A yayin haka kuma, Kakakin na shugaba Buhari ya yi watsi da rahotanni na cewar soke zaman majalisar zantarwa na mako-mako da aka saba gudanarwa sakamakon shirin shugaba Buhari na sanya hannu kan kasafin kudi.

A cewar sa Mista Adesina, an soke zaman majalisar ne a sanadiyar hutu na Bikin karamar Sallah da gwamnatin tarayya takaddamar a ranakun Juma'a da Litinin da ya shafi shirye-shiryen gudanar da zama na majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel