Shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudi 2018 gobe – Femi Adesina

Shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudi 2018 gobe – Femi Adesina

-Shugaba Muhammadu Buhari zai sanya hannu kan kasafin kudi

-Wannan na nuna cewa ya amince da abubuwan da yan majalisa suka canza cikin takardan

Bayan kimanin wata daya da majalisan dokokin tarayya suka mikawa shugaba Muhammadu Buhari kasafin kudin 2018, shugaban kasan ya shirya sanya hannu domin kasafin kudin gobe Laraba, 20 ga watan Yuni domin ya fara aiki.

Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2018 ga majalisan dokokin Najeriya a shekarar 2017 amma yan majalisan basu dawo da shi ba har sai bayan akalla wattani 6.

Shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudi 2018 gobe – Femi Adesina

Shugaba Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudi 2018 gobe – Femi Adesina

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa a goben ba za’ayi zaman majalisar zantarwa ba saboda hutun Sallan da aka samu.

Yace: “Shugaba Muhammadu Buhari zai rattaba hannunkan kasafin kudin 2018 gobe misalin karfe 12 na rana. Hakazalika gobe ba ba za’ayi taron majalisar zantarwa ba.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel