Wani babban Fasto ya bayar da N1m domin a kammala ginin Masallaci a Calabar

Wani babban Fasto ya bayar da N1m domin a kammala ginin Masallaci a Calabar

Wani babban limamin cocin Peniel Church of God, Apostle Essien Ayi, ya bayar da gudunmawar naira miliyan daya domin a kammala ginin wani Masallaci a Calabar, babban birnin jihar Rivers.

Ayi wanda dan Majalisa ne mai wakiltan wasu mazabu na Kudancin Calabar a Majalisar wakilai ya bayyana cewa, ya kamata mutanen Najeriya su dunga tallafawa junansu ba tare da la'akari da bambancin addini ba.

Faston ya bayar da wannan gudunmuwa ne a wata Mazaunar kabilar Hausawa dake birnin Calabar, inda ya ce ya yi wannan karamcin ne ne domin yabawa goyon bayan da ya samu daga gare su.

Wani babban Fasto ya bayar da N1m domin a kammala ginin Masallaci a Calabar

Wani babban Fasto ya bayar da N1m domin a kammala ginin Masallaci a Calabar

Ayi ya kuma kai ziyara wasu gidaje biyu na Marayu da kuma na tsaffi da suka gajiya inda ya malalar da dukiyar sa wajen bayar da gudunmuwa da agaji.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ya soki hukuncin gwamnatin tarayya na rufe iyakokin kasar

Ya kara da cewa, a duk lokaci da Allah ya wadata ka da arziki kai ma sai ka dubi na kasa da kai wajen taimako da bayar da tallafi.

Shugaban al'ummar Hausawa na yankin, Sarki Lawan, ya bayyana cewa wannan gudunmuwa da dan majalisa Ayi ya bayar za ta taimaka matuka wajen kammala ginin masallacin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel