Kowa ya hau motar kwaɗayi: Kotu ta yankewa wasu ƴan uwa biyu hukuncin wata 6 a dadlin satar TV plasma

Kowa ya hau motar kwaɗayi: Kotu ta yankewa wasu ƴan uwa biyu hukuncin wata 6 a dadlin satar TV plasma

- Kuruciyar bera ta kai wansu samari yan uwan juna ta baro

- Asirin samarin 'yan uwan juna da suka saci Talabijin kirar Plasma ya tonu

- Har ma an yanke musu wani hukunci biyu ciki su zabi guda

A yau Talata wata kotun majistire dake zamanta a jihar Kaduna ta yankewa wasu matasa biyu ƴan uwan juna hukuncin wata 6 kowannensu a gidan yari bisa kamasu da laifin satar TV Plasma guda biyu.

Kowa ya hau motar kwaɗayi: Kotu ta yankewa wasu ƴan uwa biyu hukuncin wata 6 a dadlin satar TV plasma

Kowa ya hau motar kwaɗayi: Kotu ta yankewa wasu ƴan uwa biyu hukuncin wata 6 a dadlin satar TV plasma

Ƴan uwan biyu Aminu mai shekaru 18 da Ibrahim 20 dukkaninsu mazauna unguwar Kawo ta jihar Kaduna sun amsa aikata laifin a gaban kuliya amma sun nemi sassauci.

Kotun ta same su ne da laifuka ukun da ake tuhumarsu da su waɗanda suka haɗa da; haɗin baki wajen aikata laifi da haurawa gida da kuma sata kayan mutane.

Alkalin kotun mai shari'a Ibrahim Emmanuel bayan yanke hukuncin ya kuma sassauta musu ta hanyar ba su zaɓin su biya tarar Naira N5,000 kowannensu kasancewar sun amsa laifinsu ba tare da wahalar da kotun ba.

KU KARANTA: Satar kujerun Coci ya sanya wani mutum kwanan gidan yari

Sannan mai shari'ar ya gargade su da su guji maimaita laifi irin makamancin wannan da zai kai ga jefa su cikin matsala.

Tun farko dai ɗan sanda mai gabatar da kara sufeto Leo Joseph ne ya gurfanar da su gaban alkalin, inda ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun aikata laifin ne a a gidan wanda yayi ƙararsu Abdullahi Danhausawa ranar 16 ga watan Fabarairu da misalin 12:0 pm na dare a unguwar kawo ta jihar Kaduna.

Joseph shaida cewa duka su biyun ne suka haɗa baki wajen haurawa gidan wani mai suna Abdullahi Danhausawa sannan suka saci TV Plasma da kudinta zai kai 130,000 tare da wasu wayoyin hannu guda uku da da zasu kai N150,000 da kuma kuɗi Naira N20,000.

A cewar ɗan sandan laifukan sun saɓa da sashi na 59 da 117 da kuma 178 na kundin tanadin dokar jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel