Yansandan Najeriya sun yi ma wasu gagararrun yan bindiga shigo shigo ba zurfi

Yansandan Najeriya sun yi ma wasu gagararrun yan bindiga shigo shigo ba zurfi

Rundunar Yansandan jihar Bayelsa ta sanar da samun nasarar cafke wani gagararren dan bindiga a jihar Bayelsa, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ya nuna.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, DSP Asinim Butsawat ne ya sanar da haka a ranar Talata, 19 ga watan Yuni, inda yace sun kama mutumin ne bayan wani amfani da dabarun aikin Yansanda a wani Otal dake garin Ekenfa, a Yenagoa.

KU KARANTA: Ido ya raina fata: Wani tsoho da ya watsa ma budurwa ruwan guba ya gamu da hukuncin Kotu

Kaakakin yace sun kwato bindigu guda uku, guda kirar AK 47, da kananu kirar Barreta daga hannunsa, inda ya shaida musu cewa yana siyar da AK 47 akan kudi naira dubu dari biyar, yayin da yake siyar da Barreta akan kudi naira dubu dari biyu da hamsin.

DSP Bustwat ya kara da cewa sun dade suna dakon wannan dan bindiga, har sai da suka shirya masa tuggun shigo shigo ba zurfi, inda suka yi badda kama kamar zasu siya bindiga a hannunsa, hakan ne ya sanya shi zuwa Otal din da suka yi ram da shi.

Kaakakin yace sun kama Dan bindigar ne tare da wani mutumi mai shekaru 34 dan asalin garin Oboro na jihar Delta, wanda shi ke kai masa masu siyan makamai daga hannunsa. Inda shi ma wanda ake tuhumar ya bayyana ma Yansanda cewa daga kasar Kamaru yake siyo makaman nasa.

Daga karshe Kaakaki Bustwat yace Yansanda ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun kwato dukkanin makaman dake hannun mutane ba akan ka’ida ba, kamar yadda bababn sufetan Yansandan Najeriya ya bada umarni.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel