Ido ya raina fata: Wani tsoho da ya watsa ma budurwa ruwan guba ya gamu da hukuncin Kotu

Ido ya raina fata: Wani tsoho da ya watsa ma budurwa ruwan guba ya gamu da hukuncin Kotu

Wata Kotun Majistri dake garin Ile-Ife na jihar Osun ta yanke ma wani Dattijo hukuncin zaman gidan Kurkuku sakamakon tuhumar da ake yi masa na yunkurin kashe wata budurwa, kamare yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ana tuhumar Adegboye Emmanuel mai shekaru 72 da laifin yunkurin kashe wata budurwa mai suna Veronica Abayomi ta hanyar watsa mata ruwan guba a fuskanta da sauran sassan jikinta.

KU KARANTA: Wani dan kwallon kasar Masar ya yi watsi da lambar yabo da wata kamfanin giya ta ba shi

A yayin zaman Kotun na ranar Talata, 19 ga watan Yuni, duk kokarin da lauyan wanda ake kara yayi na ganin Kotu ta bada belinsa ya ci tura, inda daga bisani Alkali Isola Omisade ya umarci Yansanda dasu tasa keyar wanda ake kara zuwa Kurkuku, sai ta neme shi.

Da fari, Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Emmanuel Abdullahi ya shaida ma Kotu cewa wannan tsoho ya aikata wannan aika aika ne a ranar 6 ga watan Yuni da misalin karfe 9 na safiya, a gida mai lamba 111 titin Ondo na garin Ile Ife.

Dansanda Abdllahi ya nunashe da Kotun cewa wannan laifi da Tsoho ya aikata ya ci karo da sashi na 320 (2) da 338 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Osun, don haka ya bukaci Kotun ta yanke masa hukuncin da ya dac da shi.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkali Ishola ya umarci lauyan wanda ake kara ya rubuto bukatar neman belin tsoho Emmanuel a rubuce, daga karshe y adage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Yuli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel