Gangamin zaben APC: An soke ‘yan takara 19

Gangamin zaben APC: An soke ‘yan takara 19

A daidai lokacin da gangamin Jam’iyyar APC na kasa ke gabatowa, jam’iyyar ta soke ‘yan takarar mukamai daban-daban har su goma sha tara.

Kwamitin da Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha ke jagoranta ne ya soke ‘yan takarar.

Ya kuma bayyana cewa wasu masu korafi su 18 sun rubuta koke-kokensu su ga kwamitin.

Rochas ya yi wannan jawabi ne a yayinda kwamitin sa ke wa zantawa da manema labarai.

Gangamin zaben APC: An soke ‘yan takara 19

Gangamin zaben APC: An soke ‘yan takara 19

Ya ce amma har yanzu ba a karbi wani korafi a kan mukamin dan takarar shugabancin jam’iyya ba da dan takarar Sakataren Jam’iyya na Kasa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya sharewa matasa fagen hawa kujerar mulki

Sai dai kuma Darakta Janar na Muryar Najeriya (VON), kuma jigo a cikin jam’iyyar APC, Osita Okechukwu, ya ce Rochas Okorocha ba shi da ikon soke takarar kowane dan takara. Ya ce doka ko kundin jam’iyya bai baiwa kwamitin Rochas wannan karfin ikon ba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Abiola Ajimobi yace ba zai marawa ministan sadarwa, Adebayo Shittu baya ba a kokarinsa na maye gurbinsa a matsayin gwamnan jihar Oyo.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin wata hira da Channels TV shirin Roadmap 2019 wato ‘tafiyar zaben 2019’, wanda aka gudanar a daren ranar Litinin.

Duk da cewar gwamnan da ministan wandatuni ya bayyana kudirinsa na takarar gwamnan jihar a 2019 yan jam’iyyar APC ne, gwamnan na ganin bai cancanci hawa wannan matsayi ba.

Da aka tambaye shi ko zai marawa Mista Shittu baya Ajimobi ya amsa da a’a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu domin samun ingantattun labarai:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel