Satar kujerun Coci ya sanya wani mutum kwanan gidan yari

Satar kujerun Coci ya sanya wani mutum kwanan gidan yari

- Neman samun banza ta hanyar satar abin wani ya zamo sandiyyar tafiyar wani mutum gidan yari bayan asirinsa ya tonu

- Sun haura wata Coci ne don ganin zai fi sauki suyi satarsu

Wata kotun majistire dake zamanta a jihar Legas a yau Talata ta ingiza keyar wani dan kasuwa mai suna Olaleye Olatola zuwa gidan kaso kafin yanke hukunci.

Satar kujerun Coci ya sanya wani mutum kwanan gidan yari

Satar kujerun Coci ya sanya wani mutum kwanan gidan yari

Dan sanda sufeto Abiola Olawale ya bayyanawa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne tun ranar 29 ga watan Mayu a cocin dake dake lamba 1 kan titin Oluwaseyi St. Alagbado.

Ya kara da cewa Olatola da shi da wani ne suka haura su kayi satar kujerun mallakar Pasto Smith Olusegun, wanda ya kafa cocin.

Laifin a cewarsa ya saba da sashi na 311 da 287 da kuma 411 na kundin manyan laifuka na jihar Legas na 2015.

KU KARANTA: Hatsarin mota ya hallaka mutane 11 a titin Katsina zuwa Jamhuriyar Nijar

Wanda ake zargin Olatola mazaunin unguwar 949 titin Legas/Abekuta a Alagbado ana zarginsa ne da laifuka har guda uku, cin amana da haura gidan mutane da kuma sata.

Tuni dai alkalin kotun mai suna M. I. Salami ne ya bayar da umarnin ingiza keyarsa gidan yari bayan da Olatola din ya amsa laifinsa na haurawa Cocin ta Mountain of Fire da kuma sace kujerunsu har 24 da kudinsu ya kai N50,000.

Mutukar dai kotun ta tabbatar da laifin, sashi na 311 ya tanadi hukuncin shekaru 7 a gidan yari bisa haurawa da yin sata wurin bauta, yayin da sashi na 411 ya tanadi hukuncin shekaru 2 a gidan yari.

Sanan ya dage sauraren karar zuwa karshen 26 ga watan Yuni domin cigaba da sauraren shari’ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel