Shehu Sani ya soki hukuncin gwamnatin tarayya na rufe iyakokin kasar

Shehu Sani ya soki hukuncin gwamnatin tarayya na rufe iyakokin kasar

Sanata Shehu Sani dake wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar ya soki hukuncin gwamnatin tarayya na rufe iyakokin kasar saboda safarar shinkafa yar waje.

Ministan gona da raya karkara, Cif Audu Ogbeh ya bayyana hakan a yayinda yake jawabi ga matasa a zauren shuwagabanci karkashin Guardian of the National International. (GOTNI) dake Abuja.

Shehu Sani ya soki hukuncin gwamnatin tarayya na rufe iyakokin kasar

Shehu Sani ya soki hukuncin gwamnatin tarayya na rufe iyakokin kasar

Dan majalisar ya wallafa a shafinsa na twitter, “Ba daidai bane rufe iyakokin kasa saboda safarar shinkafa’. Ya kamata ace jami’an tsaron mun sun magance ayyukan yan fasa kauri ba tare da halaka kasuwancin halali ba."

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin tarayya tace zata rufe iyakar Najeriya da makwafciyar kasar a kwanaki kalilan masu zuwa don gujewa shigo da shinkafar kasar waje cikin gida Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Kulle boda don hana shigo da shinkafa yayi daidai – Inji manoman shinkafa

Ogbeh, wanda bai fadi kasar ba da iyakar ta, yace, rufe iyakar ya zama dole domin karfafa noman shinkafa da zai riqe kasar.

Ministan yace wata makwafciyar kasa ta ci alwashin durkusar da tattalin arzikin kasar nan ta hanyar hana samar da shinkafar gida, don haka dole ne a rufe iyakar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel