Da dumin sa: Dakarun soji sun yi nasarar gungun wasu ‘yan ta’adda a jihar Benuwe

Da dumin sa: Dakarun soji sun yi nasarar gungun wasu ‘yan ta’adda a jihar Benuwe

- Dakarun hukumar soji, runduna ta 93 sun yi nasarar kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar ta’addanci ne da suka dade suna tayar da hankula da mutane a yankin Katsina Ala da kewaye

- Binciken hukumar soji ya gano cewar ‘yan ta’addar na aike ne tare da wata babbar kungiyar ta’addanci da wani Mista Gana ke jagoranta

- Hukmar sojin takara nanata kiran da ta saba yi ga jama’a da suke gaggauta sanar da hukuma a kan duk aiyukan ‘yan ta’adda ko motsin mutane da basu yarda da su ba

Dakarun hukumar soji, runduna ta 93 sun yi nasarar kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar ta’addanci ne da suka dade suna tayar da hankula da mutane a yankin Katsina Ala da kewaye. An kama su ne bayan samun bayanan sirri.

Amakaman da aka samu a hannun ‘yan ta’addar sun hada da; karamar bindiga daya, wata bindigar gida guda daya, carbi bakwai na alburusai da sauran su.

Da dumin sa: Dakarun soji sun yi nasarar gungun wasu ‘yan ta’adda a jihar Benuwe

Dakarun soji

Binciken hukumar soji ya gano cewar ‘yan ta’addar na aike ne tare da wata babbar kungiyar ta’addanci da wani Mista Gana ke jagoranta. Saidai shugaban kungiyar, Mista Gana, ya tsere amma hukumar sojin ta ce tana bin duk hanyoyin da zata iya domin ganin ta cafko shi.

DUBA WANNAN: Gaskiya tayi halin ta: Hukumar soji ta farke layar wasu ‘yan siyasa dake saka a yi kisa su dora a kan makiyaya

Hukmar sojin takara nanata kiran da ta saba yi ga jama’a da suke gaggauta sanar da hukuma a kan duk aiyukan ‘yan ta’adda ko motsin mutane da basu yarda da su ba a kan lokaci domin daukan mataki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel