Golan Najeriya da yace shekarunsa 19 na bikin dansa dan shekaru 17

Golan Najeriya da yace shekarunsa 19 na bikin dansa dan shekaru 17

- Golan Najeriya. yace shekarunsa 19 ne kacal yayin takarar uwa gasar Koin Duniya

- An gano ashe dansa ma shekarunsa 17 da haihuwa

- A yanzu yana Rasha yana fafatawa a gasar

Golan Najeriya da yace shekarunsa 19 na bikin dansa dan shekaru 17

Golan Najeriya da yace shekarunsa 19 na bikin dansa dan shekaru 17

Francis Uzoho, Golan Najeriya a bana a gasar kofin duniya dake Rasha, wanda yace shi shekarunsa 19 kacal, yanzu haka yana bikin cikar dansa da ya haia don ya cika shekaru 17 da haihuwa, ko ta yaya aka haihu a ragaya?

Akasin da aka samu, ya taya dansa murnar cika shekaru 17 ne a shafinsa na fesbuk, sai dai kash, ashe an kama har an kwape, kafin yayi maza ya goge.

DUBA WANNAN: Abubuwa 12 da ya kamata ku sani kan matatar Dangote

Golan na Najeriya, Dan shekaru 19 a duniya na murnar ranar zagayowar Dan shi mai shekaru 17,kamar yanda wani rubutun shi a Facebook ya nuna.

A wani rubutu da yayi a Facebook wanda babu dadewa ya goge, Francis ya rubuta kalaman jinjina ga Dan shi Michael. Ya rubuta :"Ina murna yau Dana na biyu, Michael ya cika shekaru 17. Ina mishi fatan albarkar Ubangiji gareshi. Yaro, mahaifinka na sonka".

Golan da qila ya manta shekarun shi 19 a duniya kuma bai kamata a ce yana da da na biyu mai shekaru 17,yayi maza ya goge rubutun.

Abokan shi dai na Facebook na ta taya shi murna, tare da fatan alheri ga Michael da kuma fatan shima shekarun shi bazasu tsaya cak a 19 ba, fatan zasu wuce hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel