APC 2019: Shin za'a tafi da OSinbajo a karo na biyu kuwa?

APC 2019: Shin za'a tafi da OSinbajo a karo na biyu kuwa?

- Mataimakin shugaba Buhari yace gwamnatinsu tana kan daidai

- Shugaba Buhari na neman tazarce a badi karkashin APC

- APC ta kafa gwamnati ne bisa doriyar chanji

APC 2019: Wannan tsarin da gwamnatin mu ke kai yana tafiyar da Najeriya kan daidai - Osinbajo

APC 2019: Wannan tsarin da gwamnatin mu ke kai yana tafiyar da Najeriya kan daidai - Osinbajo

A lokacin da shugaba Buhari ya baiwa uban tafiyar siyaar kasar Yarabawa wuka da nama, don tafiyar APC a zabukan 2015, Tinubun, ya hadiye bukatarsa ta auren siyasa da Buhari, don addinin su ya zo daya da dan takarar.

Wannan tasa dole Jagaban, ya dauko babban yaronsa Pastor Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya zaamar da shakku da Kiristoci da ma PDP ke yi na cewa wai ai Buharin na da ajandar Musuluntar da Najeriya.

DUBA WANNAN: Golan Najeriya shekarunsa 19

Sai dai yanzu, ko shugaba Buharin zai tafi da Osinbajon a karo na biyu, ko kuwa a'a?

Zai iya tafiyar dashi, amma kuma ya ajje shi a tsaka da zangon, ya dauki Bola Tinubun domin karasa wa'adinsa karo na biyu.

Ko dai ma menene, yawan jama'ar da uka yi a'am da tafiyar Faresan da Buhari sun sami kwanciyar hankali, ta yadda Farfesan ya cika aikinsa a lokutan da yake mukaddashi, ba kasala babu cin amana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel