Abinda kasar Amurka ta fada a kan harin da Boko Haram ta kai Damboa daren Asabar

Abinda kasar Amurka ta fada a kan harin da Boko Haram ta kai Damboa daren Asabar

Kasar Amurka tayi alla-wadai da harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai garin Damboa ta jihar Borno ranar Asabar da daddare tare da kasha mutane da yawa.

A jawabin da kasar Amurka ta saki tab akin kakakin hukukmar tsaron kasar, Heather Nauert, ta ce tana tare da gwamnatin Najeriya a yakin da take yi da aiyukan ta’adadanci.

Rahotanni sun bayyana cewar a kalla an yi asarar rayuka 32 yayin da wasu 84 suka samu raunuka daban-daban yayin harin da ‘yan kunar bakin wake 6 suka kai garin na Damboa dake jihar Borno.

Abinda kasar Amurka ta fada a kan harin da Boko Haram ta kai Damboa daren Asabar

Heather Nauert

Wannan harin da aka kai kan farar hula yayin da suke bikin ranar sallah ya tabbatar mana da cewar masu kai harin basu da imani ballantana ayi tsammanin samun su da tausayi. Wannan abun bakinciki ne da ban haushi,” a cewar jawabin Nauert.

DUBA WANNAN: An sake gano wasu biliyoyi da aka sace jibe a wani banki

Kazalika jawabin ya kara da cewar, “Gwamnatin kasar Amurka na tare da Najeriya ayakin da take yi da aiyukan ta’addanci.”

Kasar ta Amurka ta mika sakon tan a nuna alhini da juyayi ga iyalin da suka rasa wani na kusa das u ko wani nasu ya samu rauni sakamakon kai harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel