Rikici: Rayuka 2 sun salwanta yayin kallon 'Kwallon 'Kafa ta gasar Kofin Duniya

Rikici: Rayuka 2 sun salwanta yayin kallon 'Kwallon 'Kafa ta gasar Kofin Duniya

Wani sabon rahoto da sanadin shafin jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, wasu mutane biyu 'yan gudun hijira daga kasar Sudan ta Kudu sun rasa rayukan su yayin wani rikicin kabila da ya afku su na tsaka da kallon kwallon kafa ta gasar kofin duniya.

Hukumar 'yan sanda ta kasar ta bayyana cewa, wannan lamari ya afku ne yayin da 'yan gudunn hijirar biyu ke kallon wasan na kwallon kafa a kwatin talabijin a yankin Tika dake mazaunar 'yan gudun hijira ta sasanin Rhion.

Cikin sanarwar kakakin hukumar 'yan sanda ta jihar, Josephine Angucia, ta bayyana cewa an kashe wasu mutane biyu 'yan kabilar Dinka yayin wani rikici da kabilar Nuer da ya barke su na tsaka da kallon wasan kwallon kafa na gasar kofin duniya.

Angucia ta bayyana cewa, wannan rikici ya barke ne tsakanin kabilun biyu sakamakon cacar baki a ranar Lahadin da ta gabata wanda har ya kai zuwa safiyar ranar Litinin.

Rikici: Rayuka 2 sun salwanta yayin kallon 'Kwallon 'Kafa ta gasar Kofin Duniya

Rikici: Rayuka 2 sun salwanta yayin kallon 'Kwallon 'Kafa ta gasar Kofin Duniya

Legit.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu jami'an tsaro na 'yan sanda sun ci gaba da matsa bincike domin cafke masu hannu cikin wannan aika-aika kamar yadda Kakakin ta bayyana.

KARANTA KUMA: Masari ya yi alkawarin bayyana Lissafin Kudade na yadda yake tafi da al'amurran Jihar Katsina

Ta ci gaba da cewa, ofishin Firai Ministan Kasar ya bayar da umarnin gaggauta raba kabilun biyu na 'yan gudun hijira domin sauya masu sansanai daban-daban da zai taimaka wajen dakile afkuwar hakan a lokuta na gaba.

Rahotanni sun bayyana cewa, Kasar Sudan ta ta shiga cikin rikici tun tsawon shekaru shidda da suka gabata da ya janyo munanan tashe-tashen hankula a kan mutane da ya haifar da matsaloli na gudun hijira a babban mataki.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, akwai kimanin mutane miliyan daya 'yan Kasar Sudan ta Kudu da su ka yi hijira zuwa makociyar Kasa ta Uganda tun gabanin watan Dasumba na shekarar 2013.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel