Yan sanda sun karyata harbin mutane 4 a Kano

Yan sanda sun karyata harbin mutane 4 a Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano ta karyata rahoton kafar yada labarai dake cewa jami’anta sun harbi mutane hudu a Shoprite dake babban kantin Ado Bayero Kano a ranar 17 ga watan Yuni.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, SP Magaji Majiya sannan aka gabatarwa manema labarai a Kano a ranar Talata.

A cewarsa, ayyukan gina shataletalen da akeyi daga Dangi zuwa hanyar Zoo Road a Kan ya haddasa yawan cinkoso inda hakan ya tursasa rufe guraren shakatawan dake yankin.

Ya kuma bayyana cewa wasu matasa sun yi zanga-zanga akan rufe wajen, inda suke ta jifa da duwatsu da kuma lalata kayayyakin gwamnati, inda ya zama dole yan sanda su sanya baki domin daidaita lamura.

Yan sanda sun karyata harbin mutane 4 a Kano

Yan sanda sun karyata harbin mutane 4 a Kano

Ya kuma jaddada cewa yan sandan sun yi abunda ya kamata a lokacin da rikicin ya barke ba tare da sun harbi kowa ba.

KU KARANTA KUMA: Hotuna: Tinubu ya hadu da Atiku a filin jirgin sama na Akure

Ya kuma kara da cewa basuyi amfani da ko wani makami ba ko barkonon tsohuwa basu fesa ba.

Majiya ya bayyana cewa mutanen Kano sun yi bikin karamar Sallah cikin kwanciyar hankali inda mutane suka tafi sauran wajajen shakatawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel