Mun kosa ranan 24 ga Yuni yayi domin mu fara tuki da kanmu – Matan kasar Saudiyya

Mun kosa ranan 24 ga Yuni yayi domin mu fara tuki da kanmu – Matan kasar Saudiyya

Wasu mata a kasar Saudiyya a yau Talata sun bayyana cewa sun kosa kuma sun shirya tsaf domin zuwan ranan 24 ga watan Yuni da za’a fara basu daman tuki da kansu.

A watan Satumban 2017, sarki Salman ya alanta cewa za’a soke dokar haramtawa mata a kasar Saudiyya daman tukin mota da kansu da aka dade ana amfani da shi a masarautar.

Zaku tuna cewa yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, ya kawo sauye-sauyen zamani kasar tun lokacin da aka alantashi a matsayin yarima.

Matasa da dama a kasar sun bayyana cewa nadashi a matsayin yarima wani dama ne ga matasa wajen jin dadin rayuwa da kuma musharaka cikin al’amuran shugabanci.

Wata mata yar kasar mai suna, Amira Abdulgader, ta ce ranan 24 ga watan Yuni ranan farin ciki ne da canji kuma akwai mutum daya da zata fara yawo da ita a mota.

"A ranan 24 ga Yuni, zan so in je gidan mahaifiyata in fita yawo da ita. Tuki da daina na nufin cewa ke ce da ikon motar. Inda daman zuwa inda naga dama, abinda naga dama da kuma lokacin da naga daman dawowa” Tace

Wannan abu dai ya janyo cece-kuce tsakanin masu ra’ayin addini a fadin duniya.

Yarima mai jiran gado ya baiwa mata daman kallon kwallon kafa a fili, ya halalta gidan kallon Sinima, kana ya zurfafa abokantaka da turawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel