Mun shirya tsaf domin ficewa daga APC – Shehu Sani

Mun shirya tsaf domin ficewa daga APC – Shehu Sani

Watanni bayan shugaba Buhari ya nada Asiwaju Tinubu a matsayin shugaban kwamitin sulhun jam’iyyar APC, har yanzu jirgin sulhun bata kai ga wasu ba irinsu sanata Shehu Sani.

Sanatan wanda ya kasance mai hamayya da gwamnan jiharsa, Nasir El-Rufa’I, ya yi bayani ga manema labarai a gidansa da ke Kaduna ranan Litinin.

Yace jam’iyyarsa ta APC tana yi abubuwan da take sukan PDP da yi kafin ta hau gwamnati kuma idan ba’a dau mataki ba zasu fice daga jam’iyyar.

KU KARANTA:

Yace: “Mutane irina wadanda ba zamu yarda da rashin adalcin da ke faruwa ba. Muna jiran shugabannin jam’iyyar a sama su samo mafita amma idan basu samu mafita ba cikin makonni masu zuwa, zamu fada muku jam’iyyar da zamu koma.”

“Ina tabbatar muku da cewa mun shirya tsaf domin barin APC kuma zamu fita ne domin ba zamu lamunci rashin mutunci ba, muna baiwa jam’iyyar lokaci.”

Kan tambayan cewa shin zai iya cin zabe idan ya bar jam’iyyar APC, Shehu Sani yace: “Inada tabbacin cewa duk jam’iyyar da nayi takara zan lashe zabe. Ina da tabbacin haka. Tunda mutanen da za suyi zabe sune jama’a kuma sun daow rakiyar ‘SAK’.”

A karshe yace za’a ilmantar da jama’a cewa su zabi mutane ba jam’iyya ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel