Kulle boda don hana shigo da shinkafa yayi daidai – Inji manoman shinkafa

Kulle boda don hana shigo da shinkafa yayi daidai – Inji manoman shinkafa

- Mutane da yawa na ganin baiken yunkurin hana shigo da shinkafa da gwamnatin tarayya ke shirin yi

- Amma manoman shinkafa na kasa na ganin abu ne da ya kamata

- A cewarsu hakan zai kara musu kwarin gwuiwar cigaba da noma shinkafar a kasa baki daya

Kungiyar manoman shinkafa na kasa ta (RIFAN) yabawa shirin gwamnati na hana shigowa da shinkafa kasar nan kwata-kwata, domin a cewarta hakan zai basu kwarin gwuiwar cigaba da dukufa noman ka’in da na’in.

Kulle boda don hana shigo da shinkafa yayi daidai – Inji manoman shinkafa

Kulle boda don hana shigo da shinkafa yayi daidai – Inji manoman shinkafa

Wannan yabo ya biyo bayan kalaman da ministan aikin gona da cigaban karkara Audu Ogbeh yayi na cewa gwamnatin tarayyar zata kulle duk mashigar shigo da shinkafa kasar nan. Kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.

KU KARANTA: Gwamnatin kasar Swiss ta dawo wa Najeriya da dala miliyan $370

Shugaban kungiyar Aminu Goronyo ya bayyana cewa, idan har anyi hakan to tabbas gwamnatin tarayyar zata rage kudaden da ake kashewa wajen shigo da kaya daga kasashen ketare tare da kuma bawa manoman cikin gida kwarin gwuiwar aiki sosai.

Baya ga illar da hakan ke da ita ga tattalin arzikin kasar nan, ‘yan Najeriya sun dade suna cin shinkafar da aka ajiye ta tsawon lokaci ta hanyar sanya mata magunguna wanda hakan kan haifar da cututtukan cutar daji da sauransu. Goronyo ya jaddada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel