Adebayo Shittu bai cancanci zama gwamna ba – Ajimobi

Adebayo Shittu bai cancanci zama gwamna ba – Ajimobi

Gwamna Abiola Ajimobi yace ba zai marawa ministan sadarwa, Adebayo Shittu baya ba a kokarinsa na maye gurbinsa a matsayin gwamnan jihar Oyo.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin wata hira da Channels TV shirin Roadmap 2019 wato ‘tafiyar zaben 2019’, wanda aka gudanar a daren ranar Litinin.

Duk da cewar gwamnan da ministan wandatuni ya bayyana kudirinsa na takarar gwamnan jihar a 2019 yan jam’iyyar APC ne, gwamnan na ganin bai cancanci hawa wannan matsayi ba.

Da aka tambaye shi ko zai marawa Mista Shittu baya Ajimobi ya amsa da a’a.

Adebayo Shittu bai cancanci zama gwamna ba – Ajimobi

Adebayo Shittu bai cancanci zama gwamna ba – Ajimobi

Sai dai duk da hakan gwamnan yace shi bas hi da wani mugun nufi akan ministan, sannan yace shi ra’ayin shi ya bayyana amma idan Shittu ya ga zai iya toh ga fili ga mai doki.

KU KARANTA KUMA: Gobara ya tashi a kasuwar Bauchi inda shaguna 500 suka kone kurmus

Ajimobi ya jaddada cewa ya fadi iya gaskiyarsa akan lamarin cewa Shittu bai cancanta ba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai gana da mambobin sabuwar jam'iyyyar PDP ba (nPDP) duk da barazanar da su keyi na cewa za su fice daga jam'iyyar ta APC.

Sunyi zargin cewa an mayar da su saniyar ware a jam'iyyar ta APC kuma muddin ba'a basu damar da ganawa da shugaba Muhammadu Buhari ba, za su dauki matakin sauya sheka zuwa wata jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel