Wasu dalibai 2 daga jami'ar Najeriya sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi

Wasu dalibai 2 daga jami'ar Najeriya sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi

Wasu dalibai biyu daga jami'ar tarayyar ta fasaha da ke garin Akure babban birnin jihar Ondo watau Federal University of Technology, Akure (FUTA), masu sunayen Taofeek Olalekan Afeez da kuma Alayande Abdulwaheed Abiola sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi.

Kamar dai yadda muka samu, na'urar da suka kirkiro ta samu nasarar lashe masu gasar kirkire-kirkire da kamfanin nan na fasahar zamani na Microsoft ya saka a Najeriya.

Wasu dalibai 2 daga jami'ar Najeriya sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi

Wasu dalibai 2 daga jami'ar Najeriya sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi

KU KARANTA: Sarki Sanusi ya goyi bayan wani dan takara ba Buhari ba

Legit.ng ta samu cewa daliban biyu da ke karatun digirin su na farko a fannin ingjiniya sun kirkiro na'urar da za ta iya rage hatsarin kamuwa da cutar daskarewar jini a jikin dan adam.

Yanzu dai daliban za su wakilci Najeriya ne inda za su sake karawa da wasu mutanen daga kasashe akalla 28 a dukkan fadin duniya domin gwabzawa da nufin lashe kayautar makudan kudaden da suka kai dala dubu dari.

A wani labarin kuma, Akalla guraben ayyuka dubu 5 ne da dari 212 'yan Najeriya suka rasa a cikin watanni shida na karshen shekarar 2017 da ta gabata wanda shine yakawo jimillar yawan ayyukan da aka rasa ya zuwa dubu 10 da dari 291 a shekarar.

Wannan alkaluman dai kamar yadda muka samu, kungiyar masu kamfanonin sarrafa kayayyaki ta Najeriya ce mai suna Manufacturers Association of Nigeria, MAN ta sanar da hakan a cikin wani rahoto da ta fitar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel