Gwamnatin tarayya ta tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen saboda tsoron harin ISIS

Gwamnatin tarayya ta tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen saboda tsoron harin ISIS

Gwamnatin tarayya ta tsaurara matakan tsaro wajen tantance fasinjoji, kayayakinsu da wasu hanyoyin tun farkon wannan watan saboda barazanar sabbin hare-hare da kungiyar 'yan ta'adda na Islamic State of Iraq and Syria (ISIS) ta yi.

Duk da cewa hukumomin tsaro ba suyi karo da wani alaman harin ba, rahotanni da aka bayar na cewa mayakan ISIS da aka kora daga Iraq da Syria da sauran kasashen gabas ta tsakiya suna shigowa Najeriya abu ne da ya isa ya sanya a tsaurara matakan tsaron a filayen jiragen saman.

Gwamnatin tarayya ta tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen saboda tsoron harin ISIS

Gwamnatin tarayya ta tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen saboda tsoron harin ISIS

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ce ba zai gana da mambobin nPDP ba, ya bayar da dalilinsa

Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ne ta sanar da hukumar kula da zirga-zirgan sama ta kasa (NCAA) da hukumar kula da filayen jiragen sama na tarayya (FAAN) da kuma hukumar kula da shige da fice na kasa Kwastam game da baranar wanda ISI ta fitar a ranar 25 ga watan Afrilun 2018.

"Duk da cewa bisa ga dukkan alamu ISIS ta fi mayar da hankalinta a kan kasashen nahiyar turai, hijirar da tsaffin mayakan ISIS keyi daga Syria da Iraq da kuma kasancewar kungiyar Boko Haram na da alaka da ISIS wani abu ne da zai sa mu kara tsaurara matakan tsaro," kamar yadda ya ke a sakon da aka aike ranar 25 ga watan Mayu.

Mai magana da yawun kungiyar ISIS, Abu Hassan Al-Muhajir ya bayar da sanarwa a ranar 22 ga watan Afrilu cewa kungiyar tana wani shiri don ganin "an zubar da jini a sararin samaniya" a cikin sabon tsarin ta'addancin da suka bullo dashi.

An yada sakon a kafafen yadda labarai da yanar gizo

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel