Gwamnatin kasar Swiss ta dawo wa Najeriya da dala miliyan $370

Gwamnatin kasar Swiss ta dawo wa Najeriya da dala miliyan $370

- Ministan Shari'a na kasa Abubakar Malami ya ce gwamnatin Abacha ta ajiye makudan kudade har dala Miliyan $500 a asusun kasashen waje

- Amma a yanzu gwamnatin kasar Swiss ta dawo wa Najeriya da dala miliyan $370

A jiya ne gwamnatin tarayya ta gana da wasu wakilan kasashen Ingila and kuma Amurka domin tattaunawa don ganin yadda za a dawo da wasu kudade da aka ajiye karkashin gwamnatin Abacha daga kasar Amurka wanda sun kai kimanin dala miliyan $500.

Gwamnatin kasar Swiss ta dawo wa Najeriya da dala miliyan $370

Gwamnatin kasar Swiss ta dawo wa Najeriya da dala miliyan $370

Taron ya samu halartar manyan mutane daban-daban wadanda suka hada da Ministan Shari'a na kasa Abubakar Malami, sai kuma babban jami'i mai wakiltar Najeriya a kasar Ingila George Oguntade sai kuma sauran lauyoyi da gwamnatin Najeriya ta wakilta domin ganin an yi mai yiyuwa wajen ganin komai ya tafi daidai domin dawo da kudin.

Idan ba a manta ba kasar Amurka ta saka doka akan kudaden da gwamnatin Abacha ta kai ta ajiye a kasashe daban-daban amma yanzu haka tana da muradin cire wannan doka baya ga biyo bayan zama da kuma tattaunawa da Najeriya ta yi da kasar ta Amurka da sauran kasashen don ganin an maido da kudaden domin amfanar su.

Malami ya bayyanawa Jaridar vanguard a wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shi cewa, yanzu haka Najeriya ta amince domin sanya hannu a takadar yarjejeniyar da aka kulla domin ganin an dawo da makudan kudaden.

KU KARANTA: Hotunan motar miliyan 7 da wani dan Najeriya ya siyawa budurwar dankon sa

Ministan ya ce "Zaman da muka yi a yanzu mun duba yarjejeniyar ne kuma mun amince da komai dake ciki domin dawo da kudaden dake kasashen Ingila, Amurka da kuma Jersey, abinda ya rage kawai shi ne a watan Yuli zamu cike ragowar takardun da suka rage sannan sai a bamu kudin a dunkule".

Gwamnatin kasar Swiss ta dawo wa Najeriya da dala miliyan $370

Gwamnatin kasar Swiss ta dawo wa Najeriya da dala miliyan $370

"Gwamnatin Najeriya tana yin kokarin ganin duk wasu kudi da aka sata aka kai kasashen waje ta dawo da su domin ganin an amfanar da shi ga al'ummar Najeriya, yanzu dai komai yana tafiya daidai kuma zamu duk abinda ya kamata wajen ganin an cimma nasarar dawo da duk wani kudi da aka sata".

Yanzu dai baya ga zaman da aka yi a birnin Landan yace wakilan Najeriya zasu gana da gwamnatin kasar Switzerland, don ganin yadda za a yi wajen dawo da wasu kudade da aka sata a gwamnatin ta Abacha.

Sai dai bai bayyana ko nawa ne za a sake dawo da su ba, amma yace akwai wasu kudaden da sun kai dala miliyan $370 da gwamnatin Abacha ta boye da tuni an dawo da su zuwa babban bankin kasa (CBN) daga kasar Swiss.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel