Mace mai kamar maza: An kara samun 'yar takarar shugaban kasa a zaben 2019

Mace mai kamar maza: An kara samun 'yar takarar shugaban kasa a zaben 2019

Wata mace mai kamar maza mai suna Princess Oyenike Oyedele Roberts 'yar asalin Najeriya amma da ke da zama a kasar Amurka ta fito ta bayyana ra'ayin ta na sake tsayawa takarar shugabar kasar Najeriya a zabe mai zuwa.

Kamar yadda muka samu dai, 'yar takarar ta kuma bayyana cewa za ta nemin tikitin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ne.

Mace mai kamar maza: An kara samun 'yar takarar shugaban kasa a zaben 2019

Mace mai kamar maza: An kara samun 'yar takarar shugaban kasa a zaben 2019

KU KARANTA: PDP ta zayyana sharudda 17 ga masu neman tikitin takarar ta

Legit.ng ta samu cewa Oyenike Oyedele din take kaddamar da bukatar ta na fitowa takarar a bainar magoya bayan ta a garin New York, ta nesanta kanta da aikata cin hanci da rashawa kowane iri wanda tace shine babban jarin ta.

A wani labarin kuma, Fitaccen sarkin nan na Kano kuma babban masani a harkokin tattalin arziki Muhammadu Sanusi na II ya bayyana cewa tabbas Kingsley Moghalu ya cancanci ya iya jagoranta Najeriya a matsayin shugaba.

Sarki Sanusi dai ya bayyana hakan ne a fadar sa ta Kano a lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar shugabancin kasar da ya kai masa ziyarar ban girma a ranar Asabar din da ta gabata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel