Shugaba Buhari ya ce ba zai gana da mambobin nPDP ba, ya bayar da dalilinsa

Shugaba Buhari ya ce ba zai gana da mambobin nPDP ba, ya bayar da dalilinsa

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai gana da mambobin sabuwar jam'iyyyar PDP ba (nPDP) duk da barazanar da su keyi na cewa za su fice daga jam'iyyar ta APC.

Sunyi zargin cewa an mayar da su saniyar ware a jam'iyyar ta APC kuma muddin ba'a basu damar da ganawa da shugaba Muhammadu Buhari ba, za su dauki matakin sauya sheka zuwa wata jam'iyyar.

Mambobin nPDP din ta kunshi 'yan siyasan da suka fice daga jam'iyyar PDP suka shigo APC don marawa tafiyar shugaba Muhammadu Buhari baya kuma sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da shugaban kasan ya yi a zaben 2015.

Shugaba Buhari ya yi burus da batun tattaunawa da 'yan nPDP

Shugaba Buhari ya yi burus da batun tattaunawa da 'yan nPDP

KU KARANTA: 'Tsanar da ka liqa wa mahaifina ita za ta karka' - Diyar Janar Abacha ga Farfesa Soyinka

An gano a jiya cewa shugaba Buhari ya shaidawa shugabanin jam'iyyar APC cewa ba zai halarci ganawar da za'ayi da shugabanin nPDP din ba saboda matsalar ce ta jam'iyyar kuma ba zai yi katsalandan a ciki ba.

An ruwaito cewa shugaba Buhari ya fadawa gwamnonin jam'iyyar APC a taron da su kayi dashi cewa shugabanin jam'iyya na jihohi ne ya kamata su warware matsalolin da nPDP ta gabatar kuma idan akwai bukatar shugabanin jam'iyya na kasa za su saka baki.

An kuma ruwaito cewa shugaba Buhari ya yabawa kokarin da mataimakinsa Yemi Osinbajo ya yi na yin sulhu a batun inda ya bukaci shi ya cigaba da kokarin tattaunawar da su.

Magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari ciki har da gwamnoni suna ta gudanar da tauruka don ganin cewa an dinke dukkan matsalolin da suka kunno kai a jam'iyyar.

Sai dai su mambobin nPDP har yanzu suna barazanar ficewa daga jam'iyyar saboda wasu bukatu da suke son a biya musu. Babu tabbas cewa 'yan nPDP din za su hallarci taron kasa na jam'iyyar APC din ganin yadda suka rika ikirarin cewa ba'a damawa dasu a jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel