Gwamnatin tarayya ta sake gano wasu makudan biliyoyi da aka boye

Gwamnatin tarayya ta sake gano wasu makudan biliyoyi da aka boye

Wani kwamitin bincike na musamman (SPIP) da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa karkashin jagorancin Okoi Obono-Obla, ya binciko wasu makudan kudi, dalar Amurka miliyan $2.1 (kimanin biliyan N2.1), da aka boye a bankin Heritage.

Obono-Obla, shugaban kwamitin, ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa shugaba Buhari bayanin nasarar da kwamitin binciken (SPIP) ya samu tunda aka kafa shi.

A wata sanarwa da sakatariyar kwamitin, Lucie-Ann Laha, ta raba ga manema labarai ta ce , Obono-Obla ya shaidawa shugaba Buhari cewar, kwamitin ya gano wasu miliyan N533 da kuma wani hamshakin fili da kudin sa ya kai biliyan N1.5 daga hukumar bankin NEDIM da ta gabata.

Gwamnatin tarayya ta sake gano wasu makudan biliyoyi da aka boye

Wasu daga cikin kudin da aka gano a wani gida dake Ikoyi a Legas

Kazalika kwamitin ya kwato tare da mayar da wasu kudi, miliyan N24, da ake zargin wasu tsofin darektocin hukumar wasanni da yin awon gaba das u.

Kwamitin ya kara gano wani makeken kango, da kudin sa ya kai biliyan N2, mallakar hukumar al’adu ta kasa tare da kwatowa da mayarwa hukumar tashar jiragen ruwa wani sashe na Otal din Agura da dama mallakin ta ne.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa nake farinciki da binciken da EFCC ke yi min – Babachir David Lawal

Bayan lissafa wasu motoci masu tsada da kwamitin ya ce ya gano a hannun wasu tsofin kwamishinoni a hukumar kidayan jama’a, kwamitin ya bayyana cewar ya gurfanar da wani tsohon darekta a ma’aikatar lantarki, aiyuka da gidaje , a gaban kotu bayan ya ki bayyana dukiyar da ya mallaka.

Kwamitin ya bayyana cewar yana binciken wasu tsofin gwamnoni da ‘yan majalisu da kuma wasu kamfanoni da suke zargin anyi amfanin das u wajen wawure dukiyar al’umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel