Marayu da yan gudun Hijira sun samu sabbin gidaje 200 daga hannun Dangote

Marayu da yan gudun Hijira sun samu sabbin gidaje 200 daga hannun Dangote

Hamshakin attajiri Aliko Dangote ya kaddamar da wasu sabbin gidaje guda 200 da ya gina ma yan gudun hijira, musamman matan da suka rasa mazajensu a hannun Boko Haram, da kuma kananan yara da rikicin ya mayar dasu marayu.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito kimanin shekaru biyu da suka gabata ne Dangote yayi wannan alkawari, inda ya cika shi a yanzu, kamar yadda ya bayyana a ranar Litinin, 18 ga watan Yuni a jihar Borno a yayin kaddamar da gidajen.

KU KARANTA: Abin ya zo: Laftanar janar Buratai ya kaddamar da fadan karshe akan Boko Haram

“A shekaru biyu da suka wuce na dauki wannan alkawari a yayin wata ziyara da na kai sansanin yan gudun hijira, manufar wannan abin alheri shi ne don tallafa ma kokarin da gwamnati ke yi na sake gina ma yan gudun hijira gidajensu da yan Boko Haram suka lalata.

Marayu da yan gudun Hijira sun samu sabbin gidaje 200 daga hannun Dangote

Dangote

“Da wannan ne bayan tattaunawa da gwamnatin jihar, sai muka samar da kayan gini da suka hada da siminti, kwanukan rufi, karafan rodi, silin, winduna da Kofofi da suka kai na naira biliyan 1. Gidajen nan 200 na yan gudun hijira ne, kuma zasu dauki iyali guda

“Bugu da kari gwamnatin jihar ta samar da cibiyoyin koyar da sana’o’I ga yan gudun hijirar duk a tsakanin gidajen, haka zalika gwamnatin jihar ta gina makaranta don amfanin marayu da kananan yara.” Inji shi.

Duk da wannan namijin kokari da Dangote yayi, daga karshe yace gidauniyarsa ta kashe baira biliyan bakwai wajen yi ma yan gudun hijira hidima, kuma zai kara kashe musu kudi naira biliyan 2, don inganta rayuwarsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel