Ba zan je Amurka ba - Atiku

Ba zan je Amurka ba - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya karyata rahoton cewa zai je kasar Amurka a cikin wannan watan.

A karshen makon da ya gabata rahotanni sun nuna cewa Mista Atiku zai yi Magana a wani taron kasuwanci da zuba jari a Washington D.C a wannan watan.

An lissafa sunan Atiku cikin manyan mutanen da aka gayyata domin wannan taro.

Gwamna Nyesom Wike da Ibrahim Dankwambo, mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu da kuma ministan kasuwanci da jari, Okechukwu Elelemah na daga cikin mutanen da ake ce an gayyata.

Ba zan je Amurka ba - Atiku

Ba zan je Amurka ba - Atiku

“Babu wata gayyata makamanciyar haka ga tsohon mataimakin shugaban kasar,” kakakinsa, Pal Ibe ya sanar da majiyarmu a ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: 2019: Makarfi ya fito takarar shugaban kasa

Ya jadadda cewa basu da masaniya kan wata gayyata sannan kuma cewa basu san yadda akayi sunansa ya cika lissafin ba.

Idan dai bazaku manta ba ana zargin kasancewar Atiku cikin wata badakala inda ake zargin an hana shi shiga kasar ta Amurka sakamakon hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel