Gwamnatin Buhari ta fi sauran gwamnatoci aiki da gaskiya – Enang

Gwamnatin Buhari ta fi sauran gwamnatoci aiki da gaskiya – Enang

Babban hadimi Shugaba Muhammadu Buhari a kan harkokin majalisar Dattawa, Ita Enang, ya bayyana cewa gwamnatin Buhari na daga cikin gwamnatocin da suka fi aiki da gaskiya a kasar nan.

Enang ya yi wannan kalami ne yayin da Kungiyar Lauyoyin Jihar Akwa-Ibom ta kai masa ziyarar ban girma a babban birnin tarayya.

Ya yi kira ga lauyoyin da kuma daukacin al’umman Najeriya su rika tuntubar jami’an gwamnati kansu tsaye, a kan duk wani lamari na gwamnati da ba su fahimta ba, ko kuma su ke neman karin bayani a kai.

Ya ce yin haka shi ne mafi muhimmanci, maimakon a rika tafiya a na yi wa gwamnati mummunar fahimta.

Gwamnatin Buhari ta fi sauran gwamnatoci aiki da gaskiya – Enang

Gwamnatin Buhari ta fi sauran gwamnatoci aiki da gaskiya – Enang

Dangane da zargin da wasu ke yi cewa gwamnati na kokarin dabaibaye majalisar tarayya, Enang ya ce wannan zargin ma ga duk wanda ya san abin da ya ke yi, to ba abin kamawa ba ne.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Wata kungiyar al’umman Igbo mai suna Igbo Zuru Mee ta ce yan Bdigbo bazasu marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a 2019 ba har sai ya ba su hakuri.

KU KARANTA KUMA: Kaduna 2019: Zan kara da El-Rufai – Shehu Sani

Kungiyar tace hakurin da suka nemi ya bayar na yakin basasa ne wanda yayi sanadiyan mutuwar dubban mutanen Igbo.

Kungiyar ta kara da cewa shugaban kasar ya ba jihohin kudu maso gabas biyar naira biliyan 100 a matsayin diyya sannan kuma ya kaddamar da ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin tunawa da dukkanin wadanda suka mutu lokacin yakin basasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel