Sharhi: Batutuwa da ke tasowa daga batun Saraki da yadda aka yi fashin Offa

Sharhi: Batutuwa da ke tasowa daga batun Saraki da yadda aka yi fashin Offa

- Siyasar Bukola Saraki na iya rugujewa muddin masu laifi suka shafa masa kashin kaji

- An gano cewa ashe yaransa ne suke muggan laifuka a jihar Kwara

- Sai dai yace ba shi da masaniyar ayyukan nasu, suma sunce ba shi ya saka su ba

Sharhi: Batutuwa da ke tasowa daga batun Saraki da yadda aka yi fashin Offa

Sharhi: Batutuwa da ke tasowa daga batun Saraki da yadda aka yi fashin Offa

A baya dai, ana sa rai Bukola Saraki na da tagomashin siyasa a tsakiyar Najeriya, ganin cewa yankin na iya samar da shugaban kasa, kuma a yanzu suna da kujera ta ukku a kasar nan, musamman ganin shi bafillace ne kuma bayarabe.

Sai dai an sami wasu bayanai da aka tatsa daga wasu 'yan fashi wadanda suka yi kashe-kashe da fashi da makami.

Sabbin bayanai sun nuna cewa, duk da bai da hannu a kashe-kashen, amma dai akwai alaka mai karfi tsakaninsa da su, inda har kudaden jagaliya yakan biya su.

Motocin ma dai da suka yi fashin dasu, da sunansa a kan lambobinsu, kuma a gidan gwamnatin jihar aka boye su bayan fashin na Offa.

DUBA WANNAN: Za'a rufe iyakokin kasar nan

An kuma sami wasu cikin ma'aikatan jihar daga fadar gwamnati, suna mara musu baya, a kan aika-aikar tasu da ma jagaliyar siyasa.

Ko dai kotu ta wanke shi, ko kuwa 'yansanda su wanke shi, ko kuwa wannan shine karon karshe da za'a ji duriyar likitan da yayi wa APC juyin mulki a majalisa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel