Gwamnatin zata rufe iyakokin kasar nan, nan da 'yan kwanaki

Gwamnatin zata rufe iyakokin kasar nan, nan da 'yan kwanaki

- Shigo da shinkafa ya kara zafafa saboda ribar yin hakan

- Akwai makabartar da ake kira ta 'shahidan shinkafa' da ake harbe wa a Sahara

- Ana kokarin farfado da noman abinci musamman shinkafa

Gwamnatin zata rufe iyakokin kasar nan, nan da 'yan kwanaki

Gwamnatin zata rufe iyakokin kasar nan, nan da 'yan kwanaki

Gwamnatin tarayya tace zata rufe iyakar Najeriya da makwafciyar kasar a kwanaki kalilan masu zuwa don gujewa shigo da shinkafar kasar waje cikin gida Najeriya.

Ministan noma da raya karkara, Chief Audu Ogbeh, ya bayyana hakan a ranar litinin a Abuja, yayin da yake magana da matasa a zauren shuwagabanci karkashin Guardian of the National International.

Ogbeh, wanda bai fadi kasar ba da iyakar ta, yace, rufe iyakar ya zama dole domin karfafa noman shinkafa da zai riqe kasar.

Ministan yace wata makwafciyar kasa ta ci alwashin durkusar da tattalin arzikin kasar nan ta hanyar hana samar da shinkafar gida, don haka dole ne a rufe iyakar.

DUBA WANNAN: Noman shinkafa ya arzurta Najeriya

Ministan yace zaku ga abubuwa da dama akan rufe iyakar da zamuyi a yanar gizo. Zamuyi haka ne domin kare ku, mu da kuma tattalin arzikin kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel