Wata mata mai shekara 24 ta raunata mutane 2 da reza yayinda take ihun 'Allahu akbar' a kasar Faransa

Wata mata mai shekara 24 ta raunata mutane 2 da reza yayinda take ihun 'Allahu akbar' a kasar Faransa

Wata mata mai shekara 24 wacce ke yawo tana ihun Allahu akbar ta raunata mutane biyu a wani babban kasuwa dake kasar Faransa a ranar Juma’a 17 ga watan Yuni.

Matar ta yanki daya daga cikin mutanen ne akan kirjinsa. Sai dai dan sandan dake kara akan mutumin da aka kaiwa hari, Bernard Marchal, ya fadawa manema labarai cewa yankan baiyi muni ba.

Haka zalika harin ya cika da wata mata dake aiki a kofar fita daga kasuwan. An dauki mutanen biyu zuwa asibiti. Ana dai zaton matar na da tabin hankali.

Matar da ta kai hari ta kasance sanye da bakaken kaya sannan ta sanya bakin madubin ido. Ma’aikatan wajen tare da taimakon wasu kwastamomi biyu sun kaita wajen yan sanda.

Wata mata mai shekara 24 ta raunata mutane 2 da reza yayinda take ihun 'Allahu akbar' a kasar Faransa

Wata mata mai shekara 24 ta raunata mutane 2 da reza yayinda take ihun 'Allahu akbar' a kasar Faransa

Da aka tambayeta dalilinta na aikata hakan, bata bayar da amsa ba amma ta kasance cikin tsoro sannan kuma alamu sun nuna bata san abunda ya sha kanta hart a aikata hakan ba.

KU KARANTA KUMA: Kano 2019: Yadda za’a tabbatar da zaben lumana – Sarki Sanusi

Yan sanda sun binciki gidanta domin gano ko tana da alaka da kungiyar yan ta’addan Musulmi sai dai basu ga komai game da hakan ba tukuna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel