Kaduna 2019: Zan kara da El-Rufai – Shehu Sani

Kaduna 2019: Zan kara da El-Rufai – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya ya kaddamar da kudirinsa na takara inda zai kara da gwamnan jihar Kaduna mai ci, Mallam Nasir El-Rufai, a zabe mai zuwa na 2019.

Haka zalika anyi zargin cewa Sani ya ba da haske akan kudirinsa na barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

An kuma yi zargin cewa Sanatan yace mutane da dama da suke ganin jam’iyyar APC na muzguna masu sun fara tattara yanasu-yanasu domin barin jam’iyyar.

Sani yace jam’iyyar APC a yanzu tana kan turban rashin adalci ga mambobinta, inda ya kara da cewa jam’iyyar ta gaza cika alkawarinta na tafiya kan damokradiyya.

Sanatan ya kuma ce shi da sauran mambobin jam’iyyar bazasu amince da rashin adalci ba, inda yace idan ba’a magance matsalolin dake APC ba a makonni masu zuwa, babu ja a kudirinsa na brin jam’iyyar cikin aminci.

Kaduna 2019: Zan kara da El-Rufai – Shehu Sani

Kaduna 2019: Zan kara da El-Rufai – Shehu Sani

Da yake jawabi ga manema labarai da suka kai masa ziyarar Sallah a Kaduna, Sanatan yace zai tsaya takarar gwamnan jihar sai dai idan masu ruwa da tsaki a siyasar Kaduna wanda shima mamba ne suka ki amincewa da hakan.

KU KARANTA KUMA: 2019: Kungiyar yan Igbo sun bukaci Buhari ya basu hakuri idan har yana so su zabe shi

A bangare daya, Legit.ng ta rahoto cewa Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bukaci Gwamna Abdullahi Ganduje da ya kira wani taro na shugabannin siyasa domin shirya yadda za’ayi zaben 2019 cikin lumana a jihar.

Sarki Sanusi yayi wannan roko ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuni a wajen Hawan Nassarawa, inda a wannan hawa ne sarki ke kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel