Dan shekara 22 ya yiwa mahaifiyarsa duka har lahira saboda ta ki amincewa da soyayyarsa da kanwarta

Dan shekara 22 ya yiwa mahaifiyarsa duka har lahira saboda ta ki amincewa da soyayyarsa da kanwarta

Wani mutum mai shekara 22, Agaezichi Ogbonna, ya kashe mahaifiyarsa akan soyayyar dake tsakaninsa da kanwar mahaifiyar tasa a garin Akpaa Mbato, yankin Obingwa na jihar Abia.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wata majiya daga iyalan sun bayyana cewa Agaezichi na soyayya da kanwar mahaifiyarsa.

Don haka mahaifiyarsa, Blessing ta gargade shi akan haka inda ta bayyana hakan a matsayin abun ki a kasar Igbo.

An rahoto cewa marigayiyar ta hadu da masoyan biyu a gida sannan ta gargade su da su janye daga lamarin soyayya, amma sai Agaezichi ya far mata da duka har sai da ta mutu.

Dan shekara 22 ya yiwa mahaifiyarsa duka har lahira saboda ta ki amincewa da soyayyarsa da kanwarta

Dan shekara 22 ya yiwa mahaifiyarsa duka har lahira saboda ta ki amincewa da soyayyarsa da kanwarta

A lokacin da suka ga cewar matar ta mutu sai masoyan suka tsere, amma daga baya mata suka kama Agaezichi inda suka mika shi ga tashar sojoji dake garin.

Wani soja da ya nemi a boye sunansa, yace an mika mai laifin ga yan sanda.

KU KARANTA KUMA: 2019: Kungiyar yan Igbo sun bukaci Buhari ya basu hakuri idan har yana so su zabe shi

Da aka tuntubi kwamandan yan sanda na yankin, Aba, ACP Peter Opara ya tabbatar da cewar mai laifin na tsare a hannun yan sanda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel