Kano 2019: Yadda za’a tabbatar da zaben lumana – Sarki Sanusi

Kano 2019: Yadda za’a tabbatar da zaben lumana – Sarki Sanusi

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bukaci Gwamna Abdullahi Ganduje da ya kira wani taro na shugabannin siyasa domin shirya yadda za’ayi zaben 2019 cikin lumana a jihar.

Sarki Sanusi yayi wannan roko ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuni a wajen Hawan Nassarawa, inda a wannan hawa ne sarki ke kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar.

“Muna da roko guda ga wamnan akan tsaro. Muna rokon gwamna da ya gayyaci dukkanin shugabannin jam’iyyun siyasa domin ganin yadda za’a gudanar da zabe mai inganci cikin lumana.

Kano 2019: Yadda za’a tabbatar da zaben lumana – Sarki Sanusi

Kano 2019: Yadda za’a tabbatar da zaben lumana – Sarki Sanusi

“Ya kuma kamata mutane su sani cewa kiran yan siyasa karkashin lema guda domin daidaita al’amura ta yadda zasu inganta ba yana nunfin kiran mutane su koma wata jam’iyyar siyasa bane.

KU KARANTA KUMA: 2019: Kungiyar yan Igbo sun bukaci Buhari ya basu hakuri idan har yana so su zabe shi

“Ba hakamuke nufi ba. Kawai muna son mutane masu halin dattako su jagoranci zabe na haskiya da kuma lumana.” Inji sarkin.

A halin da ake ciki, Wata kungiyar al’umman Igbo mai suna Igbo Zuru Mee ta ce yan Bdigbo bazasu marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a 2019 ba har sai ya ba su hakuri.

Kungiyar tace hakurin da suka nemi ya bayar na yakin basasa ne wanda yayi sanadiyan mutuwar dubban mutanen Igbo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel