2019: Kungiyar yan Igbo sun bukaci Buhari ya basu hakuri idan har yana so su zabe shi

2019: Kungiyar yan Igbo sun bukaci Buhari ya basu hakuri idan har yana so su zabe shi

Wata kungiyar al’umman Igbo mai suna Igbo Zuru Mee ta ce yan Bdigbo bazasu marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a 2019 ba har sai ya ba su hakuri.

Kungiyar tace hakurin da suka nemi ya bayar na yakin basasa ne wanda yayi sanadiyan mutuwar dubban mutanen Igbo.

Kungiyar ta kara da cewa shugaban kasar ya ba jihohin kudu maso gabas biyar naira biliyan 100 a matsayin diyya sannan kuma ya kaddamar da ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin tunawa da dukkanin wadanda suka mutu lokacin yakin basasa.

Jagoran kungiyar, Cif Goddy Ike, ya fadawa manema labarai a Owerri cewa irin wannan karamcin zai kawo karshen duk wani fafutuwa a yankin Kudu maso gabas.

Kungiyar yan Igbo sun bukaci Buhari ya basu hakuri idan har yan so su zabe shi

Kungiyar yan Igbo sun bukaci Buhari ya basu hakuri idan har yan so su zabe shi

Ike yace: “Yakin ya zo karshe a 1970 amma har yanzu yan Igbo na jin radadin lamarin. Abu mafi muni shine mun rasa dubban jarumanmu.

KU KARANTA KUMA: Iyalan gida daya da direba sun mutu a hatsari a jihar Kano

“Idan har Buhari ya bayar da hakuri a yau, zaku ga cewan babu MASSOB, IPOB ko kuma wani kungiyar fafutuka. Za’a binne lamarin 1966 da 1970 kamar yadda aka binne na 12 ga watan Yuni sakamakon karrama MKO Abiola da sauran mutane da akayi.”

Idan bazaku manta ba a ranar 12 ga watan Yuni ne shugaba Buhari ya karrama Abiola da karramawa mafi girma a kasar sannan ya kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Dimokradiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel