Da dumin sa: Sabon harin kunar bakin-wake ya kashe mutum 31 a Borno

Da dumin sa: Sabon harin kunar bakin-wake ya kashe mutum 31 a Borno

- An kai sabon harin kunar bakin-wake a Borno

- An kai harin nasu ne a garin Damboa dake a jihar ta Borno

- An ce akalla mutane 31 ne suka mutu

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu dai na nuni ne da cewa wasu 'yan bindigar da ba'a san ko suwaye ba amma ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne sun kai wasu hare-haren kunar bakin wake a jihar Borno dake a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Da dumin sa: Sabon harin kunar bakin-wake ya kashe mutum 31 a Borno

Da dumin sa: Sabon harin kunar bakin-wake ya kashe mutum 31 a Borno

KU KARANTA: Badakalar Naira miliyan 100: Su Rarara sun ba gwamna El-rufai da Yari hakuri

Kamar dai yadda muka samu, 'yan ta'addan dai sun kai harin nasu ne a garin Damboa dake a jihar ta Borno a ranar Asabar din da ta gabata.

Legit.ng ta samu cewa duk da dai babu cikakken bayani game da harin kawo yanzu, amma dai hukumar agajin gaggawa ta gwamnatin tarayya watau NEMA ta ce akalla mutum 20 suka mutu.

Sai dai kuma wasu rahotannin daga wasu majiyoyin sun tabbatar mana da cewa akalla mutane 31 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel