Taron gangami: Wutar cikin gida na shirin kone jam'iyyar APC kurmus

Taron gangami: Wutar cikin gida na shirin kone jam'iyyar APC kurmus

Yayin da taron gangamin jam'iyya mai mulki a Najeriya ke ta kara matsowa, rikicin cikin gida a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar na ta dada kara ruruwa musamman ma ta yadda jiga-jigan jam'iyyar ke farautar manyan kujerun jam'iyyar.

Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa yanzu haka dai rayuka sun soma baci a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar da suke ganin an mayar da su tamkar saniyar ware tare da zargin danne su da akayi a jam'iyyar.

Taron gangami: Wutar cikin gida na shirin kone jam'iyyar APC kurmus

Taron gangami: Wutar cikin gida na shirin kone jam'iyyar APC kurmus

KU KARANTA: Jiga-jigan yan siyasa 13 da Buhari ya daure a mulkin sa

Legit.ng ta samu cewa gwamnoni da dama dai na daga cikin wadan da ke ruruta wutar rikicin jam'iyyar musamman ma yadda suka danne kowa a jihar su, lamarin da kuma baya yiwa sauran 'ya'yan jam'iyyar dadi.

A wani labarin kuma, Mataimakin shugaban kungiyar nan ta tuntuba ta arewacin Najeriya watau Arewa Consultative Forum (ACF) a turance mai suna Sanata Abubakar Girei ya bayyana cewa idan dai har 'yan sabuwar PDP da suka koma APC gabanin zabukan 2019 suka fita jam'iyyar yanzu, to kashin su ya bushe.

Sanata Girei ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da wakiliyal majiyar mu ta jaridar Punch inda ya ce duk da ko kadan baya shakkar kwarewar a siyasa to amma sun sa za su fi saurin cimma burin su a jam'iyyar ta APC.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel