2019: Ana tunanin komawa mika mulki watan Octoba, maimakon May 29th

2019: Ana tunanin komawa mika mulki watan Octoba, maimakon May 29th

- Zata duba yuwuwar hada ranar damokaradiyya da ranar murnar samun yancin kai don gujewa hutun da ake samu a kasar domin yana shafar tattalin arzikin kasar

- Jibrin tace maida ranar damokaradiyya zuwa 12 ga watan yuni tamkar cire darasin tarihi ne daga darussan makarantu

- Tayi kira ga Gwamnatin da tabbatar da dokoki da aiyukan ta, ta yanda yan baya zasu mutunta ta

2019: Ana tunanin komawa mika mulki watan Octoba, maimakon May 29th

2019: Ana tunanin komawa mika mulki watan Octoba, maimakon May 29th

Tsohuwar shugaban Justice Must Prevail Party (JMPP), Dr Sarah Jibrin ta bukaci hada ranar damokaradiyya da ranar mika mulki tare da ranar bikin murnar samun yancin kai na kowace shekara.

Ranar bikin samun yancin kai 1 ne ga watan October, kuma ranar 29 ga watan Mayu wanda shine ranar damokaradiyya inda aka fara shi a 1999,ana bikin murnar damokaradiyya a duk ranar.

Amma a ranar 6 ga watan yuni, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da maida 12 ga watan yuni ranar damokaradiyya don tunawa da ranar zaben 12 ga watan yuni na 1993,wanda aka yarda cewa marigayi Chief MKO Abiola ne yaci zaben da Gwamnatin soja a karkashin mulkin Janar Ibrahim Babangida ta soke. Abinda ya jawo fushin yan Najeriya da kasashen waje, ya kuma kawo rudani a kasar na dogon lokaci.

Jibrin ta sanar da ofishin jakadancin labarai a ranar asabar a Abuja, 12 ga watan yuni. Tace jam'iyyar ta zata kara duba 12 ga watan Mayu a matsayin ranar damokaradiyya in aka zabeta shugabancin kasar.

DUBA WANNAN:

Zata duba yuwuwar hada ranar damokaradiyya da ranar murnar samun yancin kai don gujewa hutun da ake samu a kasar domin yana shafar tattalin arzikin kasar.

Jibrin tace maida ranar damokaradiyya zuwa 12 ga watan yuni tamkar cire darasin tarihi ne daga darussan makarantu.

Tayi kira ga Gwamnatin da tabbatar da dokoki da aiyukan ta, ta yanda yan baya zasu mutunta ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel