'Tsanar da ka liqa wa mahaifina ita za ta karka' - Diyar Janar Abacha ga Farfesa Soyinka

'Tsanar da ka liqa wa mahaifina ita za ta karka' - Diyar Janar Abacha ga Farfesa Soyinka

Gumsu Abacha ta cacaki fittacen marubucin Najeriya Farfesa Wole Soyinka saboda kalamen da ya fada game da mahaifinta, marigayi shugaban kasa Sani Abacha.

Gumsu ta yi rubutu a shafin sada zumunta na Facebook inda ta ce kiyayan da Farfesan ke yiwa mahaifinta ne zai yi ajalinsa a duniyar nan.

A dai makon da ya gabata ne Soyinka ya furta cewa babu yadda za'ayi shugaba Muhammadu Buhari ya karrama marigayi MKO Abiola kuma a lokaci guda ya rika yabon wanda ya soke zabensa kuma ya daure shi a kurkuku.

'Duk tsanar da ka liqa wa mahaifinmu ita zata karka' - Diyar Janar Abacha ga Farfesa Soyinka

'Duk tsanar da ka liqa wa mahaifinmu ita zata karka' - Diyar Janar Abacha ga Farfesa Soyinka

KU KARANTA: Sojin Sama sun kaiwa Boko Haram goron sallah

A jawabin da Soyinka ya yi a taron karama jarruman siyasa na Najeriya da akayi a ranar Laraba a Abuja, ya ce duk da cewa ya fahimci girmamawar da Buhari ke yiwa Abacha a aikin soja, bai dace ya bari hakan ya sha karfin daukaka demokradiyya ba.

Rubutun na Gumsu ya janyo cece-kuce tsakanin mutane da yawa a dandalin na facebook inda wasu ke ganin cewa Farfesa Soyinka yana da hujja a kan maganar da ya fadi, wasu kuma na ganin cewa shugaba Buhari yana da dalilansa na girmama Abacha.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel