Kishin-Kishin: Buhari na shirye-shiryen yin kwaskwarima a gwamnatin sa bayan sallah

Kishin-Kishin: Buhari na shirye-shiryen yin kwaskwarima a gwamnatin sa bayan sallah

Wani labarin da muke ji yana fitowa daga majiyar mu mai karfi daga fadar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na nuni ne da cewa shugaban na shirin yi wa jami'an gwamnatin sa musamman ma ministoci kakkabar 'ya'yan kadanya da zarar an kammala hutun salla.

Duk da dai cewa a iya cewa wannan ne karo na uku da shugaban ke daukar niyyar sauke wasu daga cikin ministocin sa amma yana fasawa, wannan karon an ce da gaske yake yi kuma ba wasa.

Kishin-Kishin: Buhari na shirye-shiryen yin kwaskwarima a gwamnatin sa bayan sallah

Kishin-Kishin: Buhari na shirye-shiryen yin kwaskwarima a gwamnatin sa bayan sallah

KU KARANTA: Yadda yanayin garuruwan musulmi 15 za su kasance

Legit.ng dai ta samu cewa shugaban a kwanan baya ya fada da bakin sa cewa zai sha wahala kafin ya maye gurbin daya daga cikin ministocin sa da yayi murabus kimanin sati biyu da suka shude.

Wannan ne ma dai ya sanya masu sharhi akan al'amurran mulki suke ganin cewa akwai yiwuwar shugaban ya dan yi wa ministocin nasa kwaskwarima.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel