Lauyan Evans, Ogungbeje, ya janye daga shari'a

Lauyan Evans, Ogungbeje, ya janye daga shari'a

Mun samu rahoton cewa, Olukoya Ogungbeje, Lauya mai kare shahararren mai garkuwa da mutanen nan, Chukwudumeme Onwuamadike, ya janye shari'ar sa wanda a halin yanzu take hannun babbar kotun tarayya dake jihar Legas.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, Ogungbeje ya bayar da wannan sanarwa ne yayin ganawa da manema labarai inda yake cewa ya janye daga shari'ar ne sakamakon barazana da ke yiwa rayuwar sa.

Yake cewa, da shi da sauran lauyoyi masu kare fitaccen mai garkuwa da mutanen nan da ya shahara da sunan Evans sun janye wakilcin da suke masa sakamakon yawaitar barazanar da ake yi ga rayuwar su.

Legit.ng ta fahimci cewa, bayan tsawon lokutan yana sheke ayarsa, Evans ya shiga hannun hukuma ne tun a shekarar da ta gabata bisa laifin garkuwa da mutane da ya shahara yana cin karen sa babu babbaka.

Lauyan Evans, Ogungbeje, ya janye daga shari'a

Lauyan Evans, Ogungbeje, ya janye daga shari'a

Rahotanni sun bayyana cewa, gwarzon jami'in nan mataimakinkwamishinan 'yan sanda na kasa, Abba Kyari shi ya taka rawar gani wajen jagorantar jami'an tsaro da har aka cafke wannan shu'umin mutum da ya addabi kasar nan.

A halin yanzu dai Lauya masu kare sa sun janye daga shari'ar da ke hannun babbar kotun tarayya ta jihar Legas sakamakon barazana ga rayuwar su da ake ci gaba da yi a fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: Rashin Cika Alkawari ya sanya na kashe Ubangida na Ma'akacin Sojin Ruwa da Budurwar sa

Hakazalika jagoran lauyoyi ya bayyana cewa ko kadan ba sa da na sanin wannan wakilci da suka yi na kare Evans a gaban kotu duk da irin girman laifuffuka da ya aikata gami da suka da aibatawa da suka sha a kasar nan.

Bugu da kari Ogungbeje ya na farin cikin wannan tarihi da suka kafa a kasar nan na kawowa wannan mataki na gudanar shari'ar duk da irin cin mutunci da suka ta al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel