Gwamna Yari ya yi murabus a mukaminsa na babban mai tsaron jiharsa

Gwamna Yari ya yi murabus a mukaminsa na babban mai tsaron jiharsa

Gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara ya ce ya yi murabus daga matsayinsa na babban jami'in tsaro na jiharsa saboda bashi da iko a kan jami'an tsaro dake aiki a jiharsa.

A yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a Talata Mafara a jiya Juma'a, Yari ya ce ya dauki wannan matakin ne saboda halin rashin iya tubaka komai game da game da kashe-kashen al'umma da akeyi a jihar.

KU KARANTA: Sabon salo: Shugabanin jam'iyya sunyi rantsuwa kafafu tsirara

Ya koka kan yadda duk da cewa doka ta nada shi a matsayin babban jami'in tsaro na Jiharsa, bashi da ikon daukan wasu matakai da tsare-tsare don kare rayyuka da dukiyoyin mutanen jiharsa.

Gwamna Yari ya yi murabus a matsayinsa na babban mai tsaron jiharsa

Gwamna Yari ya yi murabus a matsayinsa na babban mai tsaron jiharsa

"Mun dade muna fama da matsalar rashin tsaro cikin yan shekarun nan sai dai duk da matsayina na babban jami'in tsaro na Jihar ta, bani da ikon fadawa jami'an tsaro abinda zasuyi ko kuma hukunta su idan sunyi kuskure.

"Hasali ma, matsayin na babban jami'in tsaro kawai suna ne," inji shi.

Gwamnan ya yi juyayin yadda kashe-kashen da akeyi a Jihar suka cigaba duk da umurnin da shugaba Muhammadu Buhari ya bawa jami'an tsaro na kawo karshen zubda jini a wasu jihohin kasar nan.

A cewarsa, tun bayan umurnin da shugaban kasan ya bayar na kawo karshen kashe-kashen, har yanzu abin bai kakauta ba. A makon da ya wuce, an kai wani hari da ya yi sandaidyyar rasuwar mutane 30.

Ya ce gwamnatin Jihar na kashe makuden kudade a kan jami'an tsaro dake jihar amma kwaliya bata biya kudin sabulu ba.

Gwamna Yari ya umurci al'ummar jihar su dage da addu'oi na musamman don samun saukin kashe kashen da ke jihar.

Ya kuma yi kira da mutanen jihar su cigaba da hakuri tare da bawa gwamnati da jami'an tsaro hadin a yanzu da ake daukan matakan kawo karshen kashe-kashen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel