Ba zan mayarwa EFCC ko kwabo ba - Wani tsohon gwamnan PDP

Ba zan mayarwa EFCC ko kwabo ba - Wani tsohon gwamnan PDP

- Tsohon gwamnan Jihar Oyo, Rashidi Ladoja ya ce babu wani kudin da zai mayar wa hukumar EFCC

- Dalilinsa na fadin hakan shine tun farko dama babu kudin da ya sata saboda haka batun mayar da kudi bai taso ba

- EFCC na zarginsa da sayar da hannun jarin mallakar jihar kan farashi mai sauki tare da soke kudaden a aljihunsa

Tsohon gwamnan JIhar Oyo, Rashidi Ladoja ya ce ko kadan hankalinsa baya tashi saboda binciken da hukumar yaki da rashawa EFCC ta fara yi akansa inda ya kara da cewa babu kudin da zai mayar wa hukumar saboda bai saci ko sisi ba lokacin da yake gwamna.

Ba zan mayar wa EFCC ko kwabo ba - Wani tsohon gwamnan PDP

Ba zan mayar wa EFCC ko kwabo ba - Wani tsohon gwamnan PDP

EFCC ta gurfanar da Ladoja ne a gaban kuliya saboda zarginsa da almundahanar kudaden al'ummar jiharsa lokacin da ya ke gwamna tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007.

KU KARANTA: Ta baci: Sojoji da 'yan sanda sunyi musayar wuta

A yayin da ake fara sauraron karar, lauyan EFCC, Abubakar Madaki, ya shaidawa kotu cewa tsohon gwamnan ya bayar da umurnin a siyar da hannun jari malakar jihar wanda kudinsa ya kai N6.6 biliyan a farashi mai rahusa ba tare da ya nemi amincewar majalisar jihar ba.

Madaki ya yi ikirarin cewa wasu kusoshin gwamnati ne a wannan lokacin suka raba kudaden tsakaninsu sai dai Ladoja ya musanta wannan zargin da akayi masa.

Bayan komawarsa jam'iyyar PDP a bara, Ladoja ya sake bayyana alamun zai fice daga jam'iyyar saboda dalilan rashin jituwa dake tsakaninsa da da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP reshen jihar Oyo.

Ladoja ya ce shi da magoya bayansa sun bawa jam'iyyar wa'adin kwanaki bakwai domin su warware matsaloli da shi Ladoja da mutanensa suka yi nuni a akai idan ba haka ba kuma zasu tattare komatsensu suyi gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel