Zaben 2019: Jihar Kano ta Buhari ce - Ganduje

Zaben 2019: Jihar Kano ta Buhari ce - Ganduje

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana a ranar Juma'ar da ta gabata cewa damar da shugaban Kasa Muhammadu ke da ita a zabe mai gabatowa za ta ci gaba da kasancewa mai ban mamaki kamar yadda ta kasance shekaru da dama da suka shude.

Ganduje ya bayyana hakan ne ga tsohon gwamnan jihar Abia, Dakta Orji Uzor Kalu, yayin da ya ziyar ci fadar gwamnatin sa inda yace shugaba Buhari bai taba rashin nasarar zabe a jihar Kano ba har ta yayin da yake jam'iyyar adawa.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, shugaba Buhari bai taba rashin nasarar zabe a jihar Kano ba tun yayin da ya sanya riga ta siyasa a kasar nan. Kuma wannan nasara tana samuwa ne ko da kuwa yana jam'iyyar adawa ne sabanin ta gwamnatin jihar.

A sanadiyar haka ya sanya gwamna Ganduje ya ke kira ga shugaba Buhari akan kada ya damu kansa dangane da zaben 2019 domin kuwa in dai nasara ce ya samu ya gama a jihar Kano kasancewar su na kan sahu daya na jam'iyyar APC.

Zaben 2019: Jihar Kano ta Buhari ce - Ganduje

Zaben 2019: Jihar Kano ta Buhari ce - Ganduje

Ya ci gaba da cewa, irin soyayyar da al'umma jihar ke yiwa shugaba Buhari ba ta da misali saboda haka ba bu wani macancancin kujerar fadar Villa dake babban birnin kasar nan face shugaba Buhari.

A kalaman Ganduje, "Wannan shi yake nuna muhimmanci jihar Kano tare da Gwamnatin ta ga shugaba Buhari. Buhari shine Kano kuma Kano ta Buhari ce wanda wannan shine yaren siyasar a halin yanzu."

KARANTA KUMA: Wasu Fusatattun Mutane sun lakadawa wani Barawon Mota duka har Lahira a Jihar Anambra

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin ziyarar aiki ta yini biyu da shugaba Buhari ya kai jihar Kano watanni kadan da suka gabata, gwamnatin jihar tare da masu ruwa da tsaki suka shaida masa matakin shigar da kara har gaban kotu muddin bai sake neman takara ba a zaben 2019.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Buhari ya ketare wannan barazana yayin da ya bayyana kudirin sa na sake neman takarar kujerar sa a zaben kasa mai gabatowa.

A nasa jawaban, Orji Kalu ya bayyana cewa ire-iren masu adawa da tsayawa takara ta shugaba Buhari ba bu abinda suka nufata face ganin Najeriya ta koma wani yanayi makamanci yanayi na kafin shekarar 2015 wanda babakere da handamar kudin gwamnati ya kasance al'ada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel