Hukumar 'Yan sanda ta cafke Mutane 20 'Yan Kungiyar asiri a jihar Akwa Ibom

Hukumar 'Yan sanda ta cafke Mutane 20 'Yan Kungiyar asiri a jihar Akwa Ibom

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumar 'yan sanda ta jihar Akwa Ibom ta bayyana cewa ta cafke wasu mutane da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne da suka addabi karamar hukumar Eket ta jihar.

Shugaban hukumar reshen karamar hukumar ta Eket, Emeka Nwonyi, shine ya bayyana hakan yayin wani taro na gaggawa da akan tsaro tare da masu ruwa da tsaki a garin na Eket a ranar Juma'ar da ta gabata.

Mista Nwonyi ya bayyana cewa an cafke wannan miyagun mutane 20 a ranar Lahadi 10 ga watan Yuni da ta gabata. Ya kuma ce wannan daduma ba ta tsaya haka ba domin kuwa za su ci gaba da cafke su.

Hukumar 'Yan sanda ta cafke Mutane 20 'Yan Kungiyar asiri a jihar Akwa Ibom

Hukumar 'Yan sanda ta cafke Mutane 20 'Yan Kungiyar asiri a jihar Akwa Ibom

Yake cewa, hukumar 'yan sanda ta ƙudirta bankado masu hannu cikin wannan mugunyar laifi kuma duk ya shiga hannu zai fuskanci babban sakamakon na fushin doka.

KARANTA KUMA: Dakatar da wani Dan Majalisar Dokoki na Jihar Ekiti

Ya kara da cewa hukumar ba za ta gushe ba wajen ganin ta murkushe wannan miyagun mutane sai dai akwai hanzari ba gudu ba na neman alfarma ta al'umma akan bayar da rahotanni masu amfani da za su taimaka wajen kawar da muggan iri daga zamantakewa ta gari.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a can jihar Anambra ne wasu fusatattun mutane suka lakadawa wani Barawon Mota duka da har sai da yace masu ga garin ku nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel