Wasu Fusatattun Mutane sun lakadawa wani Barawon Mota duka har Lahira a Jihar Anambra

Wasu Fusatattun Mutane sun lakadawa wani Barawon Mota duka har Lahira a Jihar Anambra

A daren ranar Alhamis din da ta gabata wasu daruruwan fusatattun Mutane su ka lakadawa wani barawon mota duka har Lahira jim kadan bayan an gudanar da wata jana'iza a kauyen Umudike dake karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, hukumar 'yan sanda ta jihar ta yi Allah wadai da wannan hukunci na al'ummar yankin, inda suka gargade su akan kauracewa daukar hukunci na doka a hannayen su.

A yayin tabbatar da afkuwar wannan lamari a ranar Juma'ar da ta gabata, Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Mista Haruna Muhammad, ya shaidawa manema labarai a birnin Awka cewar tuni aka killace gawar wannan Mutum a dakin ajiyar gawa na wani asibitin kurkusa.

Yake cewa, fusatattun mutanen sun hau kan wannan Barawo yayin da mamallakin motar, Ifeanyi Obijiaku, ya yi yekuwar hagen motar sa kirar Honda CRV a hannun wannan Matashi yayin da yake yunkurin arcewa da ita.

Wasu Fusatattun Mutane sun lakadawa wani Barawon Mota duka har Lahira a Jihar Anambra

Wasu Fusatattun Mutane sun lakadawa wani Barawon Mota duka har Lahira a Jihar Anambra

Yake cewa, mutanen sun lakada masa duka har sai da ya fice daga hayyacin sa yayin da jami'ai masu gudanar da sintiri a yankin suka yi gaggawar mika shi asibitin Koyarwa na Nnamdi Azikiwe inda likitoci suka tabbatar da cikawar sa.

KARANTA KUMA: Mun daura Damarar magance matsalar rashin aikin yi - Osinbajo

Legit.ng ta fahimci cewa, kawowa yanzu ba bu wata masaniya kan wannan Barawo yayin da tuni jami'an yan sandan suka kammala binciken su kan motar da kuma mabudin da aka yi amfani da shi wajen bude ta.

A yayin haka kuma, hukumar ta sha alwashin damke wadanda ke da hannu wajen aiwatar da wannan mugun nufi da ya salwantar da rayuwar mutum ta wannan muguwar hanya, inda a halin yanzu bincike ya ci gaba da kan kama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel