Sabon salo: Shugabanin jam'iyya sunyi rantsuwa kafafu tsirara

Sabon salo: Shugabanin jam'iyya sunyi rantsuwa kafafu tsirara

A jiya Alhamis 14 ga watan Yuni ne Shugabanin jam'iyyar Justice Must Prevail Party (JMPP) su kayi rantsuwar kama aiki a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja kafafu tsirara.

Shugabanin Jam'iyyar ta JMPP sun ce a shirye suke don yin gwagwarmayar hambarar da shugaba Muhammadu Buhari daga kujerarsa a babban zaben kasa da za'ayi a shekarar 2019.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Dr. Olusegun Ijagbemi ya jagoranci manema labarai da sauran yan jam'iyyar zuwa harabar dakin da akayi taron kuma ya cire takalmarsa kafin ya yi rantsuwar kama aiki.

Sabon salo: Shugabanin jam'iyya sunyi rantsuwa kafafu tsirara

Sabon salo: Shugabanin jam'iyya sunyi rantsuwa kafafu tsirara

KU KARANTA: A karo na farko, mahaifiyar Shekau tayi magana a kan Boko Haram

Shugaban kwamitin amintatu na jam'iyar, Dr. Chukwuemeka Ezeife da Uwar kasa, Dr. Sarah Jibrin da Alhaji Ibrahim Mohammed suna cikin wadanda suka cire takalmansa kafin su kayi rantsuwar daukan aiki.

A lokacin da suke rantsuwar daukan aikin, dukkan mambobin jam'iyyar sunyi addu'ar cewa muddin suka ci amanan al'umma a kan rantsuwar da su kayi, toh duk abinda suka ci ya zama masu guba rayuwar su ta duniya.

A wani labarin na Legit.ng Rafiu Salau, dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) a zaben 2015 ya jadada goyon bayansa ga tazarcen shugaba Muhammadu Buhari inda ya ce babu wanda yafi dacewa ya jagoranci Najeriya fiye da Buhari.

A cewar tsohon dan takarar shugabancin kasar, Buhari ne mutum daya tilo da zai iya jagorancin Najeriya don rike matsayinta a nahiyar Afrika da duniya baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel