Saboda sabon Bacci yayin aiki, an Dakatar da wani Dan Majalisar Dokoki na Jihar Ekiti

Saboda sabon Bacci yayin aiki, an Dakatar da wani Dan Majalisar Dokoki na Jihar Ekiti

Cikin gaggawa Majalisar Dokoki ta jihar Ekiti ta bayar da umarnin dakaci na sai Mama ta gani kan wani dan Majalisar ta, Mista Sunday Akinniyi, mai wakiltar mazabar Ikere bisa sabon sa na yawaita bacci yayin da yake bakin aikin sa da kuma ta'azzara ta'addanci.

Kamar yadda shafin jaridar Sahara Reporters ya bayyana, an gargadi wannan dan majalisa akan kada ya kuskura ya sake kusantar harabar majalisar tare da shigar da korafin ga hukumomin tsaro dangane da barazana ga rayuwar mambobin ta.

A cewar shugaban kwamitin rahotanni da bayanai na majalisar Dakta Samuel Omotoso, ya bayyana cewa wannan dakaci ya zo ne a sakamakon korafe-korafe akan Akinniyi da shugaban harkokin gudanarwa na Majalisar ya shigar, Tunji Akinleye.

Omotoso ya bayyana cewa majalisar ta yanke wannan hukunci ne bayan wani kwamitin da Ayodele Fajenilehin ya jagoranta ya gabatar da binciken sa a gaban majalisar dangane da al'amurran da suka shafi dan majalisa Akinniyi.

Saboda sabon Bacci yayin aiki, an Dakatar da wani Dan Majalisar Dokoki na Jihar Ekiti

Saboda sabon Bacci yayin aiki, an Dakatar da wani Dan Majalisar Dokoki na Jihar Ekiti

Legit.ng ta fahimci cewa, binciken majalisar ya bayyana yadda a makonni kadan da suka shude Akinniyi ya fara kawo tashe-tashen hankali kan Sandar Girma ta majalisar tare da nuna munanan halayya zuwa al'ummar mazabar sa da kuma abokan aikin sa 'yan majalisa.

KARANTA KUMA: Gwamnati ta sanya takunkumin zirga-zirga da ababen hawa na tsawon sa'o'i 12 a Jihar Yobe

Rahotanni sun bayyana cewa wannan lamari ya sanya majalisar ta yanke wannan hukunci baya ga a sha ruwan tsintsaye da yake wajen halirtar zama na majalisar musamman a lokutan da ake tattauna al'amurran da suka shafi mazabar sa.

Bugu da kari Akinniyi yana da dabi da sabon yawaita yin bacci yayin zaman majalisa wanda hakan ya sanya aka yi masa lakabi da "Honarabul Mai bacci" duk da tsawatar masa da kakakin majalisar Kola Oluwawole ya sha fama.

A sanadiyar wannan cin kashi ne da rashin sanin ciwon kai ya sanya majalisar ta yanke hukunci dakatar da dan majalisar ba tare da kayyade ranar dawowar sa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel